OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar dattawa ta fara nazarin kudirin dokar daidaita daukan ma'aikata

Majalisar dattawa ta fara nazarin kudirin dokar daidaita dau

Photo Source: The Guardian

Majalisar dattawa na nazarin wani kudirin doka da zai tsara yadda ake daukar ma’aikata, masu koyo da masu horarwa da sauran bangarorin ma’aikatan Najeriya.

Dokar kuma tana neman a baiwa Hukumar Samar da Aiki ta Kasa (NDE) damar ba da lasisi da kuma sa ido kan ayyukan hukumomi masu zaman kansu a kasar.

Kudirin dokar wanda Sani Musa daga Niger ya bayyana a gaban majalisar ya tsallake mataki na biyu a ranar Laraba.

An karanto kudirin dokar a karo na biyu bayan ‘yan majalisar sun tattauna cikakkun bayanai kan dokar.

A cikin muhawarar da ya jagoranta, dan majalisar ya ce ana gudanar da ayyukan ne a kan karamin tsari tare da samar da ayyuka masu yawa wanda yawanci mallakin wasu ne.

Ya ce shigar da tattalin arzikin Najeriya ta bangaren da bai da ce ba hakan na nuna alamu ne na take hakkin ma'aikata da rashin aiwatar da ka'idojin aiki.

Aiki mai kyau shine adalci, albashi mai kyau, da yanayin aiki mai kyau, aminci da kariya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci