OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kwankwaso Ya Bayyana Dalilin Rashin Zuwa Taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya

Kwankwaso Ya Bayyana Dalilin Rashin Zuwa Taron Kungiyar Lauy

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin rashin halartar sa taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na 2022 a Legas.

Kwankwaso ya bayyana dalilin sa ne a wata wasika da ya aika wa shugaban kungiyar, Olumide Akpata kamar yadda kakakin yakin neman zabensa, Abdulmumin Jubril ya gabatar.

A cewar wasikar, Kwankwaso ya rubuta cewa: “Na rubuto ne domin amincewa da samun wasikar da kuka yi kan wannan batu da ke sama, kuma ina so in sanar da ku cewa ba zan iya halartar wannan taro mai matukar muhimmanci ba sakamakon wasu al'amura na kasa da suka rike ni. 

“A halin da ake ciki, da na aika aboki takara na, Bishop Isaac Idahosa, domin ya wakilce ni da kuma bayyana ra’ayoyin mu na sabuwar Najeriya mai ci gaba. Amma abin takaici, a halin yanzu yana kasar waje.

"Saboda haka, ina so in ba da uzurina na kasa halartar taron kuma ina tabbatar muku cewa jam'iyyar New Nigeria People's Party tana da ra'ayi daya tare da NBA game da manufarmu daya ta zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasar mu."

Ku tuna cewa Kwankwaso da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba su halarci taron ba.

Sai dai kuma Tinubu ya aika abokin takarar sa, Kashim Shettima ya wakilce shi.

Sauran ‘yan takarar da suka halarci taron sun hada da, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar; Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi da Dumebi Kachikwu na jam'iyyar African Democratic Party (ADP)

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci