OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Kungiyar Fulani Makiyaya Ta Koka Kan Takunkumin Da Gwamnatin Delta Ta Sanya musu

Kungiyar Fulani Makiyaya Ta Koka Kan Takunkumin Da Gwamnatin

Kungiyar Fulani makiyaya a Kudancin kasar nan koka bisa sabbin dokoki da gwamnatin jihar Delta ta sanya musu na hana shanun su kiwo a jihar.

A watan Satumban 2021 ne gwamnatin Delta ta sanya  ta sanya dokar hana shanu kiwo a dazukan dake jihar, wanda kuma wa’adin da jihar ta sanya zai cika a wannan wata na Fabarairu.

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen jihar Delta, Alhaji Musa Muhammad, ya ce dokar za ta hana dabbobin su sakewa, sannan za su samu matsala da masu gonaki, wanda hakan ya sanya su kullum cikin fargaba.

Ya ce dokokin da gwamnatin ta sanya musu sun yi tsauri, inda ya bayyana fatan samun samun sassauci.

''Abinda na ke nufi shi ne baki dayan jihar Delta babu wani daji, hatta gidajen da muke zaune filayen mutane ne, cikin gonaki ne da sai an zo ana cirar rogo da sauransu. Idan aka ce za a yi lissafi, a haka Shanun da suke nan, sun fi 500,000, a zo a ce ba za mu yi kiwo ba.

Dan hakan ne muke rokon gwamna yadda mu ke zaune lafiya da masu gonaki a taimaka a bar mu haka kafin abubuwa su tabarbare,'' in ji Alhaji Musa.

Ya kara da cewa daman gwamnati na kiransu da jami'an tsaro domin a yi zama, duk lokacin da aka samu wata matsala ko bullar wata fitina.

Alhaji Musa ya ce dokokin da aka kafa na cewa su tsare Shanunsu babu zuwa ko ina kiwo sun yi tsauri ga batun cin tarar Saniya da batun idan an kama su da yawa za'a biya naira 500,000.

Sannan dokar ta tanadi cewa duk wanda ya gaza biyan wanann tara zai yi zaman kason shekara 5 ko 10.

Shugaban ya ce inda kasar arewa suke, inda akwai dazuka, da wurin shan ruwa da dukkan abin da suke bukata da sauki, amma inda suke babu dazuka ko kaura za su yi babbar matsala hakan ke zame musu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci