OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jihar Nasarawa: 'Yan sanda sun kama mutum biyu da kisan wani yaro dan sati uku a duniya

Jihar Nasarawa: 'Yan sanda sun kama mutum biyu da kisan wani

Nigerian Police force

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu da suka kashe wani yaro mai sati uku a duniya a Jihar. 

Rundunar, ta bakin mai magana da yawun ta, DSP Ramhan Nansel ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

A cewar Nansel, an yi kamen ne biyo bayan rahotannin sirri bayan wadanda ake zargin sun buya. 

Wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Oktoba a Lafia, babban birnin jihar.

Kakakin rundunar a cikin sanarwar ya ce, wadanda ake zargin sun hada da Abdulkadir Ahmed mai shekaru 40 da kuma abokin sa Hassan Sabo mai shekaru 40.

Ahmed wanda shi ne uban yaron tare da abokin sa ya yaudari matar sa ​​kuma mahaifiyar yaron a kan neman sulhu.

Matar da ta same su a shagon Ahmed, sai Sabo ya jata da hira a waje yayin da babban wanda ake zargin (Ahmed) ya shiga da yaron cikin shagon.

A cewar sanarwar, yayin da mahaifiyar ke waje, sai ta ji yaron yayi kara, daga nan yayi shiru.

Nan take wanda ake zargin ya fito daga shagon ya shaida mata cewa yaron yayi bacci. 

Ana cikin haka kafin ta duba gawar dan nata, sai mutanen biyu suka tsere a kan babur.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta kai gawar zuwa Asibitin kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya domin binciken gawar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci