OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jam'iyar ADC Ta Dakatar Da Ɗan Takararta Na Shugaban Ƙasa

Jam'iyar ADC Ta Dakatar Da Ɗan Takararta Na Shugaban Ƙasa

ADC National Chairman, Ralph Nwosu in handshake with Monye

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta dakatar da Dumebi Kachikwu, dan takararta na shugaban kasa.

Dakatar war na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan Mista Kachikwu ya goyi bayan kiran da shugabannin jam’iyyar suka yi ga Ralph Nwosu, shugaban jam’iyyar na kasa da ya yi murabus.

A wata sanarwa a ranar Asabar, Bamidele Ajadi, mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa, ya ce an dauki matakin ne a taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka gudanar a ranar Juma’a.

Ajadi ya ce tun lokacin da Kachikwu ya zama dan takarar jam’iyyar, ya kasa samar da dabarun yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar wanda za'a fara nan ba da dadewa ba, ruwaitowar Jaridar TheCable.

“Kwamitin zartaswa na jam'iyar sun kalli bidiyon da ba ta da tushe balle makama, wanda Mista Dumebi Kachikwu ya wallafa kuma ya watsa shi, wanda aka yi niyya don ɓata mutunci da kima da zaman lafiya da ya shafi jam'iyar mu da jami’anta na ƙasa".

“Sun kuma lura cewa tun daga ranar 9 ga watan Yuni 2022 da aka zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa, ya gaza, ya yi sakaci kuma ya ki nuna wa jam’iyyar duk wata taswirar yakin neman zaben shugaban kasa mai ma’ana, don zaben shugaban kasa mai zuwa.

“Ayyukansa marasa kyau da/ko rashin aiki ya zuwa yanzu, sun kawo cikas ga makoma da fatan dukkan ‘yan takararmu da ke neman mukamai daban-daban a fadin kasar nan.

“Kwamitin na majalisar gaba daya, a fili kuma babu shakka ya yi Allah-wadai da wannan faifan bidiyon gaba dayansa tare da bayyana shi a matsayin wani mummunan shiri na zage-zage, don haka ya bada shawarar dakatar da shi nan take daga jam’iyyar daga yau Juma’a 2 ga watan Satumba, 2022.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci