OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Inuwa Yahaya Ya Kaddamar Da Bada Tallafin Taki Na Noman Damuna

Inuwa Yahaya Ya Kaddamar Da Bada Tallafin Taki Na Noman Damu

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da sayar da takin zamani na tallafin noma na shekarar 2022.

Gwamnan ya kaddamar da hakan ne a kauyen Dukul da ke karamar hukumar Kwami a jihar.

A yayin bikin rabon takin, gwamna Yahaya ya ce za a siyar da takin ne a kan kudi naira 19,000 kan kowacce buhu sabanin farashin kasuwa na N25,000.

Da yake mayar da martani kan dalilin da ya sa aka makara wurin rabon takin, gwamnan ya bayyana cewa matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan da kuma wasu dalilai ne suka kawo tsaikon. 

Ya yi nuni da cewa, gwamnatinsa ta samar da hanyoyin da za takin zai kai ga manoman tun daga kasa. 

Ya bayyana cewa za a raba kayan ne ta rumfunan zabe a kowace karamar hukumar jihar.

A cewar sa, “Manufar mu ita ce, mu tabbatar da cewa manoman mu na karkara sun samu dukkanin kayayyakin amfanin gona na yau da kullum a kofar gidansu ba tare da la’akari da ja-in-ja na tattalin arziki da ke da alaka a baya ba."

Gwamna Yahaya ya kuma nuna damuwar sa kan yadda manoman ke tsallakawa cikin filin da aka kayyade don kiwo.

Ya yi kira ga manoma da su daina wuce iyakan filin su yayin da ya bukaci makiyaya da su guji kiwo a gonakin jama'a.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci