OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NDLEA Ya Kama Masu Hada-hadar Kwayoyi 150 A Kaduna

Hukumar NDLEA Ya Kama Masu Hada-hadar Kwayoyi 150 A Kaduna

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA ta bayyana kama masu fataucin kwayoyi dari da hamsin, tare da rufe guraren da ake hada-hadar kwayoyin ashirin da biyar a jihar Kaduna cikin watan Agustan 2022.

Shugaban hukumar a Kaduna, Umar Adoro shi ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa hakan a safiyar yau Laraba.

Yace an rufe guraren hada-hadar a unguwannin Kudenden, da Unguwar Muazu, Unguwar Rimi. Rigasa, Karji da Unguwar Gwari.

Sauran guraren da ake siyar da kwayoyin sun hada da unguwannin Babbar saura, Gadar gayan, Mando, Badarawa, Makarfi, Azara, Iche, Karatudu da Saminaka da sauran su.

Yace cikin mutane dari da hamsin da aka kama, 6 ne kawai mata.

Adoro ya buƙaci al'ummar jihar su dinga taimakawa hukumar da bayanan sirrin da zasu basu damar kamawa tare da dakile ayyukan hada hadar miyagun kwayoyi a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci