OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Mai Sarrafa Akurkura A Kano

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Mai Sarrafa Akurkura A Kano

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta ce jami’anta sun yi nasarar cafke wani mai yin wani sabon sinadari mai kara kuzari da aka fi sani da Akuskura,mai suna Qasim Ademola.

 

Jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA sun samu Qasim din da kwalabe 26,600 na haramtaccen maganin Akurkura da aka tanada domin rabawa a fadin jihohin Arewa.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Femi Babafemi, Jami'in Hulda da jama'a na hukumar NDLEA, ya fitar a Abuja, ranar Lahadi.

 

Hakazalika,sanarwar ta ce jami’an hukumar sun kama wani tsohon mai laifin, Onyeka Charles Madukolu a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja,Legas bisa laifin shigo da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 5.90 da aka boye a cikin gwangwani turare da man leben mata.

Onyeka wanda ya shafe shekaru bakwai a gidan yari a Habasha bisa laifin safarar miyagun kwayoyi kuma bayan an sake shi ne  daga kurkuku a shekarar 2020, ya sake komawa sana'ar shi ta da aka sake kama shi a ranar Juma’a, 16 ga Satumba, 2022, a filin jirgin sama na Legas lokacin da ya dawo daga Sao Paulo, dake kasar Brazil dauke da miyagun kwayoyin.

 

 Sanarwar ta ce: ‘’A binciken da aka yi a kayansa an gano cewa ya boye hodar ibilis mai nauyin kilogiram 5.90 a cikin gwangwani Kayan kwalliyar mata. A yayin hira ta farko, ya yi ikirarin cewa ya shiga sana'ar safarar miyagun kwayoyi ne don tara sabon jari don fara kasuwancin halal bayan an sake shi daga kurkukun Habasha a 2020."

 

A cewar hukumar ta NDLEA, Onyeka dan shekaru 44 dan asalin karamar hukumar Awka ta Arewa da ke jihar Anambra ya ce yana sa ran za a biya shi Naira miliyan 2 Idan yai nasarar isar da maganin zuwa Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci