OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NDLEA ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 611 a Kaduna

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama mutane 611 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a jihar Kaduna.

Hukumar ta ce an kama mutanen ne daga watan Janairu zuwa Yuli na 2022.

Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kaduna, Umar Adoro ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau (Litinin).

Kwamandan ya bayyana cewa mutane 480 masu shan miyagun kwayoyi daga cikin mutane 611 da hukumar ta yi musu gyara sun koma mu'amala cikin al’umma.

A cewarsa: “An gurfanar da 131 a gaban kotu kuma mun samu hukuncin mutum 69 sannan 62 na dakon shari’a a cikin wa’adin bincike. 

 "A cikin wa'adin binciken, rundunar ta kuma kama haramtattun miyagun kwayoyi da suka hada da Cannabis 3,893.189kg, hodar ibilis 1.309kg, Heroin 0.097kg, Psychotropic 3,949.63kg, da Methamphetamine 0.147kg, 65kg.

"Jimlar kwayoyin da aka kama sun kai kilogiram 3,898,991.552 a cikin lokacin da ake bincike," kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Adoro ya kuma yi kira ga ’yan kasa da su tallafa wa hukumar da bayanan sirri kan kayayyakin da ake tuhuma don hana fatauci da shan miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa akwai bukatar iyaye su sanya ido sosai akan 'ya'yan su domin duba abin da suke aikatawa.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya bayar, kwamandan ya kara jaddada kudurin hukumar na tsaftace al’umma daga haramtattun kwayoyi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci