OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Hukumar Kwastam ta yi alkawarin tallafa wa masana'antun kera motoci na cikin gida

Hukumar Kwastam ta yi alkawarin tallafa wa masana'antun kera

Adewale Adeniyi, Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya, ya yi alkawarin tallafa wa motocin da ake kerawa a cikin gida, inda ya ce goyon bayan irin wannan shirin zai bunkasa tattalin arzikin kasa.

 

Ya yi wannan bayani ne yayin da ya gwada tuka motar da aka kera a masana'antar cikin gida kamar yanda jawabin da aka wallafa a shafin hukumar na X (tsohon Twitter) ya bayyana a ranar Juma’a.

 

 An ruwaito Adeniyi yana cewa, “hakki ne daya rataya akan mu mu tallafawa irin wadannan masana'antun dake kokarin samar mana da kayyayakin cikin gida saboda ba zai yiwu mu ci gaba da dogara kan abubuwan da muke shigo da su ba, musamman motoci."

 

“Don haka ne ake ta kokarin tallafa musu, an samar musu da rangwame da dama kuma hanya daya tilo da za a kara tallafa musu, ita ce ganin yadda za mu yi amfani da kayayyakinsu kuma wannan shi ne mataki na farko da muka dauka."

 

Kwanturolan kwatsam din ya tabbatar da cewar za su yi farin cikin kulla yarjejeniya da su don "abin da na gani ya burge ni sosai, na tuka motar na wani dan lokaci kuma tayi aiki yanda ya kamata" 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci