OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnan Jihar Yobe ya Kaddamar da Shaguna 600 da Rumfunan Kasuwa

Gwamnan Jihar Yobe ya Kaddamar da Shaguna 600 da Rumfunan Ka

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni|

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kaddamar da shaguna da rumfunan kasuwa 600 tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya.

 

An kaddamar da aikin ne a garin Buni Yadi dake karamar hukumar Gujba a jihar.

 

Gwamnan ya ce aikin wani mataki ne na dawo da al’ummomin da suka rasa matsugunansu kamar yadda ya alkawarta lokacin yakin neman zabe.

 

A yayin bikin kaddamar da aikin, gwamnan ya bayyana cewa samar da aikin a Buni Yadi zai taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin jama'a.

 

Ya bayyana Buni Yadi a matsayin cibiyar kasuwanci ta jihar inda ya kara da cewa shi me "dalilin da ya sa muka hada kayan aiki domin inganta rayuwar al'ummarmu".

 

Yayin da yake yaba wa abokan huldar ci gaba, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tabbatar da samar da kayayyakin amfanin gona domin inganta ayyukan noma.

 

Ya kuma bukaci wadanda suka amfana da su tabbatar da yin amfani da kayan da aka samu yadda ya kamata.

 

Da yake yaba wa gwamnan, shugaban karamar hukumar Gujba, Dala Alhaji Mala ya ce al’ummar Gujba na godiya da yadda suka shaida ribar dimokuradiyya.

 

Ya kuma bayyana cewa jama’a za su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga gwamnan bisa ga dimbin ayyukan da suka samu.

 

Ya kuma yaba wa gwamnan bisa yadda aka gyara babban asibitin Buni Yadi da sauran dakunan shan magani, gina tituna da magudanun ruwa, tallafin tsaro da dai sauransu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci