OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Bayyana Machina A Matsayin Ɗan Takaran Sanatan APC A Yobe Ta Arewa

Kotu Ta Bayyana Machina A Matsayin Ɗan Takaran Sanatan APC

Bashir Sherif Machina, Ahmed Lawan

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu ta umarci jam’iyyar APC  da hukumar zaɓe mai zaman kanta da su amince da Bashir Machina a matsayin dan takarar sanatan Yobe ta Arewa a jam’iyyar.

Mai shari’a Fadima Murtala Aminu, ta soke zaɓen fidda gwanin da aka yi wanda ya samar da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, a ranar 9 ga watan Yuni, 2022.

Alkalin ya kuma umurci APC da ta mika sunan Machina ga hukumar zaɓe a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani da aka gudanar a watan Mayu.

Hukuncin na zuwa ne makonni kaɗan bayan da Machina ya nisanta kansa daga sanarwar janyewa daga takaran.

Kwafin sanarwar da wakilin Jaridar Punch ya samu ya nuna wata wasiƙa da ake zargin Machina ya rubutawa shugaban jam’iyyar na kasa inda ya bayyana ficewa daga takarar sanatan Yobe ta Arewa.

Idan za'a iya tunawa, a ranar 9 ga Agusta, 2022, an ruwaito cewa hukumar zaɓe ta musanta amincewa da Lawan da Sanata Godswill Akpabio a matsayin ƴan takarar sanata na jam’iyyar APC.

Sanata Lawan da Akpabio duk sun fafata ne a zaben fidda gwani na shugaban ƙasa na APC.  

Sai dai bayan sun sha kaye, dukkansu biyun sun sanya jam’iyyar APC ta sanya sunayen su a matsayin ƴan takarar sanata, amma hukumar ta ƙi amincewa da su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci