OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Uwa Da Dan Ta A Kano

Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Uwa Da Dan Ta A Kano

Motar Kashe Gobara

Wata Gobara a ranar Asabar ta yi sanadiyyar mutuwar wani yaro dan shekara daya, da mahaifiyar sa a Gidan Kaji dake Titin Gwarzo a jihar Kano.

 

Sanarawar da kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar ta ce wani bawan Allah, Usman Nura ne ya kira hukumar da safiyar  Asabar din.

 

Ya ce jami’an sun yi kokarin ceto matar,  Zainab Yusha'u da dan ta, Sulaiman Usaini, sai dai sun fita hayyacin su kafin a samu fitowa da su, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwar su.

 

 Saminu Yusuf Abdullahi ya kara da cewa tuni suka mika gawarwakin ga mijin matar, Malam Usaini.

 

Yace jami’anta sun kuma yi kokarin shawo kan gobarar kafin ta tsallaka makwabtan gidaje, inda ya kuma yin kira ga al’umma da su ci gaba da taka tsan-tsan wajen amfani da wuta, musamman a wannan lokaci na sanyi domin kare afkuwar gobara.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci