OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Enugu: Al'ummar Ibagwa Nike Sun Koka Bisa Yunkurin Hana Gudanar Da Bikin Sabuwar Doya

Enugu: Al'ummar Ibagwa Nike Sun Koka Bisa Yunkurin Hana Guda

Nigerian Police

Al'ummar kauyen Ibagwa Nike dake karamar hukumar Enugu ta gabas sun koka bisa yunkurin fin karfi da Sarkin garin Igwe Emmanuel Ugwu yake musu ta hanyar amfani da Yan Sandan yankin wajen hana su gudanar da shagalin bikin sabuwar doya.

Al'ummar kauyen suna zargin Kwamishinan Yan Sandan jihar, Abubakar Lawal da Shugaban Rundunar yankin SP Eze da yin amfani da karfin iko wajen cin zarafin al'ummar kauyen.

A jawabin sa ga manema labarai, Shugaban kwamitin amintattu na kauyen Iky Ngwu ya zargi Kwamishinan Yan Sandan da yin amfani da sashin hana fashi da makami na rundunar wajen kama dukkan dattawan kauyen bisa umarnin sarkin garin duk da cewar hukuncin babbar kotun jihar ya basu cikakkiyar damar gudanar da shagalin bikin sabuwar doyar.

A nashi bangaren, Kwamishinan ƴan Sandan jihar, Abubakar Lawal yace zargin da mutanen kauyen suke mishi kazafi ne kawai saboda kyama da suke nunawa yan Sanda musamman ma sashen bincike na CID.

Shi kuwa Igwe Emmanuel Ugwu yace alumar kauyen suna yunkurin kawo baraka ne a yankin domin tun kwanakin baya aka gudanar da bikin sabuwar doyar a garin kamar yadda ake yi duk shekara. 

Ya ce hakan ne ma yasa yaga rashin dacewar basu damar gabatar da wani sabon bikin na daban kamar yadda suka bukata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci