OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Da Ɗumi-ɗumi: An Kama Mai Shiga Tsakani Da Ƴan Bindigar Da Suka Sace Fasinjojin Jirgin Ƙasa A Hanyar Kaduna, Tukur Mamu

Da Ɗumi-ɗumi: An Kama Mai Shiga Tsakani Da Ƴan Bindigar D

Jami’an tsaro sun kame babban mai shiga tsakani da yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa ranar 28 ga watan Maris a hanyar Abuja zuwa Kaduna Tukur Mamu a Cairo, babban birnin Egypt.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, am kama Tukur Mamu tare da iyalan sa ne bisa umarnin gwamnatin tarayyar Najeriya.

Rahotannin sun kuma bayyana cewa an kame Tukur Mamu ne a hanyar sa ta zuwa Umara, kafin bayan awanni 24 a dawo da shi kasar nan.

Jaridar ta Daily Trust ta ce Tukur Mamu ya shaida mata cewa ba’a same shi da wasu haramtattun kaya a yayin tafiyar sa ba duk da binciken da hukumomin kasar ta Egypt suka gudanar kan kayan da yake tafe da su a safiyar Talata.

Ya kara da cewa hukumomin kasar nan sun yi yunkurin tsare shi a wata kasar, sai dai hakan su bai cimma ruwa ba bayan hukumomin Egypt sun tabbatar da yana dauke da cikakkun takaddun tafiye-tafiye.

Tukur Mamu ya janye daga shiga tsakani da yan bindigar bayan da ya zargu gwamnatin kasar nan da barazana ga lafiyar sa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci