OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

DA DUMI-DUMI: Gobara Ta Ci Rabin Gonar Obasanjo

DA DUMI-DUMI: Gobara Ta Ci Rabin Gonar Obasanjo

Chief Olusegun Obasanjo| Hoto Daga: BBC

Gobara ta kone gonar tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo da ke jihar Benue.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Gwer inda gonar ta ke, Emmanuel Otserga ya ce sama da rabin gonar ne gobara ta cinye.

Gonar da ta kai kimanin hekta 139, ta kama da wutan ne da misalin karfe 2 na rana a ranar Asabar.

Shugaban Karamar hukumar ya bayyana cewa gobarar ta kone sama da rabin gonar a lokacin da masu kai daukin gaggawa suka iso.

Ya kara da cewa, “Daga kallon yadda abin ya faru, gobarar ta tashi ne sakamakon gangancin da ‘yan barna suka yi, domin yadda ake kiyaye gonan, babu yadda za a yi wuta ta tsallaka daga kowace bangare zuwa cikin gonar."

Otsega ya ci gaba da cewa, tuni aka kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a lamarin.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Catherine Anene yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, ta ce batun kama mutanen bai iso gare ta ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci