OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

CBN Ya Hana Bankunan Kasashen Waje Bude Ofisoshi A Najeriya

CBN Ya Hana Bankunan Kasashen Waje Bude Ofisoshi A Najeriya

Babban bankin Najeriya (CBN) ya hana bankunan kasashen waje da ke aiki da ofisoshin wakilci a Najeriya gudanar da ayyukan da aka ayyana a matsayin ‘kasuwancin banki’ da dai sauransu.

 Babban bankin ya bayyana hakan ne a a cikin rahoton ka’idojinsa na kula da ofisoshin wakilan bankunan kasashen waje a Najeriya.

 Da yake lissafta ayyukan da ba a yarda  bankunan kasashen waje da ke aiki a cikin kasar, ka'idar ta ce: "Ofisoshin Wakilai da aka amince da su ba za su shiga Waɗannan ayyukan masu zuwa ba;

Samar da ayyukan da aka keɓe a Najeriya a matsayin kasuwancin banki; Samar da duk wani aiki na kasuwanci ko ciniki wanda zai iya haifar da fitar da daftari don ayyukan da aka yi; da kuma karɓar umarni a madadin babban kamfanin dake kasar waje; da kuma shiga cikin kowace ma'amala ta kuɗi kai tsaye.''

 Sai dai, ka’idar ta CBN ta kara da cewa: “Ofisoshin wakilan bankunan kasashen waje suna da muhimmiyar manufa ta baje kolin yanayin ayyukan da bankunan da suke wakilta suke gabatarwa.

Bisa wannan dalilin, wakilan bankunan za su iya samar da hannun jarin kai tsaye daga ketare zuwa Najeriya da ke karbar bakuncinsu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci