OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Shugabannin Jami'o'i Sun Buƙaci Gwamnati Ta Sake Duba Batun Ba Aiki Ba Biya

ASUU: Shugabannin Jami'o'i Sun Buƙaci Gwamnati Ta Sake Duba

Kwamitin shugabannin jami’o’in tarayya (CVC) na jami’o’i sun roki gwamnatin Najeriya da ta sake tunani kan matakin da ta dauka na ba ‘Ba Aiki, Ba Biya’, bi sa dalilin wasu yan matsaloli da suka ​​​​​​dabaibaye kungiyoyin jami’o’in.

Kungiyar ta ce wannan tsari barnar da zata haifar ya fi gyaran da zai haifar ga jami'o'i.

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin cewa ba za ta biya ma'aikatan jami'o'i albashi ba har na tsawon yajin aikin da suke yi, tana mai cewa matakin ya yi daidai da dokokin aiki.

Sa dai kungiyoyin ma’aikata, musamman kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), sun bayyana manufar a matsayin rashin adalci da rashin kyautatawa.

ASUU ta ce aikin koyarwa shi ne mafi saukin aiki ga mambobinta, inda ta ce ya kunshi kusan kashi 10 cikin 100 na sharudan karin girma.

Kungiyar ta ce yayin da take yajin aiki, mambobinta na ci gaba da gudanar da bincike da ayyukan ci gaban al’umma.

Shugabannin jami'o'i sun roka Shugabannin jami'o'i sun ce manufar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ za ta kara haifar da barna da kuma barin dalibai zaune ba madafa Hukumar ta CVC ta kuma gargadi gwamnati game da bude jami’o’i a dole, tana mai cewa hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin jami’'o'i Sulayman Abdulkareem, farfesa kuma mataimakin shugaban jami’ar Ilorin ya fitar bayan wani taron gaggawa na kwamitin a ranar Talata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci