OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda Uku A Enugu

Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴan Sanda Uku A Enugu

Nigerian Police force

Jami’an ‘yan sanda uku ne aka kashe a daren Laraba a lokacin da ‘yan bindiga suka kai wani hari a New Haven, a jihar Enugu kudu maso gabashin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:15 na dare a tashar bas.

An ce ‘yan bindigan sun bude wa jami’an wuta, inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi.

Lamarin ya haifar da fargaba ga mazauna yankin. Wani ganau, wanda ke da shagon daukan hoto kusa da wurin da lamarin ya faru, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun auka wa jami’an ‘yan sandan ne.

“’Yan sanda uku ne an kashe, amma gawarwaki biyu kawai muka gani. Sun ce an kai daya asibiti,” inji shi.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES faruwar lamarin a safiyar Alhamis.

Ya ce jami’an na aikin sintiri ne a lokacin da ‘yan bindigar suka zo cikin wata mota kirar Lexus SUV suka far musu.

"An tabbatar da mutuwar jami'an su uku a asibiti," in ji shi. Mista Ndukwe, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce an fara farautar wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci