OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Alkalin kotun shari’ar Musulunci ya yi alkawarin biyan sadaki N100,000 ga wasu masoya

Alkalin kotun shari’ar Musulunci ya yi alkawarin biyan sad

A ranar Laraba ne Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kaduna, Salisu Abubakar-Tureta, ya yi tayin biyan sadaki Naira 100,000 don taimaka wa wani Salisu Salele ya auri burin zuciyar sa Bilkisu Lawal.

Alkalin ya bawa Salele damar ya je ya yi tunani a kan tayin da aka yi masa, ya kuma dawo ya sanar da kotu hukuncin da ya yanke a ranar 6 ga watan Satumba, ranar da aka saka don dawo wa ci gaba da sauraron karar.

Mahaifiyar Bilikisu, Rayila Lawal, ta maka Salele a gaban kotu, inda ta bukaci ta tilasta masa ya auri diyarta idan da gaske yana sonta ko kuma ya rabu da ita idan bai shirya auren ta ba.

"Muna zaune unguwa daya yana zuwa wurin diyata ba tare da neman izinin mu ba.

“Na je na sami mahaifiyarsa kan lamarin sai ta nuna min danta bai shirya aure ba.

“kawai sai Salele ya yanke zuwa zance wurin diyataya sai ya chanza dabara zuwa Kiranta a waya suna haduwa a wurare daban-daban. 

"Dan haka na yanke shawarar gurfanar da shi a kotu,'' in ji Malama Rayila.

Ta bayyana cewa a shirye ta ke ta aurar da ‘yarta idan har Salele ya shirya.

Da yake kare kansa, Salele ya ce yana son yarinyar amma bai shirya yin aure ba sai bayan shekara biyu.

“Ni dalibi ne da nake karatu a daya daga cikin jami’o’in tarayya kuma ba zan so aure yadauke min hankali ba.

"Baya ga haka, ba ni da kudin sadaki ina zaune neda iyayena,”  Salele ya shaida wa kotu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci