OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Abin da yasa Najeriya ba za ta iya halatta matatun mai ba - Kyari

Abin da yasa Najeriya ba za ta iya halatta matatun mai ba -�

Rukunin matatar man fetur na kasa ta bayyana cewa sai an inganta matatun mai in har ana so a sami abinda ake bukata.

Babban jami’in rukunin kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, Limited, Mele Kyari, ya ce Najeriya ba za ta iya halasta matatun mai na hannu ba.

Jaridar DAILY NIGERIAN  ta ruwaito cewa an yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar masana’antu da su samar da kananan kayayyakin sarrafa danyen mai domin kawar da gurbacewar yanayi a yankin Neja Delta.

Amma Mista Kyari, yayin da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Najeriya, NTA, a ranar Litinin, ya jaddada cewa ya kamata a karfafa matatun mai, maimakon a dinga tacewa ba bisa ka'ida ba.

Mista Kyari ya kara da cewa kasar ba ta da wani zabi da ya wuce ta rufe kayayyakin tacewan.

Ya ce: “shi yasa aka ba da lasisi ga matatun mai, inda su ke iya samar da ganga 1,000 zuwa ganga 20,000 a kowace rana."

“Tacewa ilimin ne mai zaman kan sa." 

Shugaban kamfanin na NNPC ya ce Najeriya na asarar bpd 700,000 saboda satar danyen man fetur da kuma rufe wuraren da ake hakowa.

Yana mai cewa: “Yana aiki ta hanyoyi biyu ,na farko shine satar mai kai tsaye sannan sai a sarrafa shi a matatun mai ba bisa ka’ida ba sannan sai a fitar da shi daga bututun mai.

"Abin da ke faruwa shi ne duk lokacin da muka sami irin wannan al'amari, mukan rufe kayan aikinmu, hakan ya kasance asara." 

Shi yasa abinda ke zuwa hannun mu ganga miliyan 1.4 ne.

"Muna da karfin iya yin miliyan 2.1.

"A zahiri muna yin asarar kusan ganga 700,000 na mai a kowace rana da ake hakowa.

"Ba ko yaushe ba ne ya ke kasancewa sata."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci