OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Yadda Kwankwaso ya yaudare mu – Shekarau

2023: Yadda Kwankwaso ya yaudare mu – Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya ce jam'iyyar NNPP ta yi musu alkawaruka shida sauran mabiyan sa,sai dai jam'iyyar ta kasa cika ko daya daga ciki.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce kungiyar sa ta yi matukar fusata da jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) saboda kin tabbatar da sharuddan yarjejeniyar da suka kulla kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar.

Malam Shekarau, wanda ya kasance dan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta tsakiya, ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, da cin amanar ‘ya’yan kungiyar sa biyo bayan sauya sheka da suka yi zuwa jam’iyyar a watan Mayu.

Kwankwaso a wata hira da aka yi da shi a Sashen Hausa na BBC ya ce jam’iyyar ta kasa biyan bukatar Malam Shekarau saboda kungiyar sa ta shigo jam’iyyar a makare lokacin INEC ta riga ta rufe bada damar kai sunayen ‘yan takara.

Kwankwaso ya kara da cewa,"a siyasa, abu ne mai wahala ace ma wani dan siyasa ya sauka ya bar wa wani".

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci