OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Ɗan Takarar Gwamnan Enugu Ya Yi Zargin Kuɗin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu Ya Kawo Hargitsi A APC

2023: Ɗan Takarar Gwamnan Enugu Ya Yi Zargin Kuɗin Yaƙin

Ɗan takarar shugaban Ƙasa a jam'iyyar APC Oka Ahmed Tinubu

Dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Enugu, Uchenna Nnaji, ya ce baza su taba kudaden da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu ya bayar ba.

Mista Nnaji ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan gano cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ya samo asali ne sakamakon kudaden yakin neman zaben da Tinubu ya aikewa jam’iyyar a jihar.

Dan takarar gwamnan, wanda ya bayyana haka a wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ofishin jam’iyyar na shiyyar Kudu maso Gabas a ranar Lahadi a Enugu, ya ce kudaden da Mista Tinubu ya bayar ya kamata kar a taba su har sai bayan zabe sakamakon hargitsi da hakan ya haifar.

“Rikicin da ke faruwa a APC kudin kamfen din da Tinubu ya raba ne ya haifar.

Masu ruwa da tsaki sune ke fafutukar ganin sun jagoranci yadda za a raba kudaden,” inji shi.

“Da yardar Allah, za mu yi amfani da dukiyar jihar Enugu wajen gudanar da zabe a 2023 bayan zabe sai jam’iyya ta mayar da mana da kudaden mu.

Kudaden kamfen din Tinubu ne ke haddasa rikici a jihar,” Mista Nnaji ya bayyana.

Ya ce zai gana da shugaban jam’iyyar na kasa da kuma Mista Tinubu domin sanar da su matakin da aka dauka.

Nnaji ya roki masu ruwa da tsaki da su dawo gida su hada kai da shi wajen goyon bayan jam’iyyar APC a Enugu domin jam’iyyar ta samu nasara a zabe mai zuwa a jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci