OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zulum ya raba gidaje ga malaman firamare 24 A Borno

Zulum ya raba gidaje ga malaman firamare 24 A Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da raba gidaje ga malaman makarantun Firamare 24 a jihar.

Gidajen na daga cikin sabbin rukunin malamai da gwamnatin Zulum ta gina.

Daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin har da wata malamar kabilar Igbo, Mrs Obiageri Mazi wadda gwamna Zulum ya taba haduwa da ita da sanyin safiya a makaranta yayin wata ziyarar ba zata da ya kai. 

Zulum ya daukaka Mazi daga matsayin malamar aji zuwa mukamin mataimakiyar shugabar makarantar a matsayin babban tukuicin ganin ta kan kiyaye lokaci.

Ta fito daga jihar Abia kuma ta kasance malama a makarantar firamare ta Shehu Sanda Kyarimi 2 da ke karkashin hukumar ilimi ta karamar hukumar Jere tsawon shekaru 31.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun samu takardun zama ne a wani karamin biki da aka gudanar a jiya a rukunin malamai da ke Bulumkutu kan titin zuwa filin jirgin sama.

Bikin ya gudana ne karkashin jagorancin kwamishinan ilimi na jihar Injiniya Lawan Abba Wakilbe.

A yayin da yake mika gidaje guda 24 cike da kaya ga malaman makarantun Firamare daga Maiduguri da karamar hukumar Jere (LEA), Wakilbe ya ce gwamnati ta yi irin wadannan gine-ginen a garin Banki da ke karamar hukumar Bama da kuma Mafa.

Wakilbe ya bukaci malaman da su kula da wurin da kyau domin dukiya ce ta hukuma.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci