OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yanzu Mata Basa Bukatar Muharrami Don Aikin Hajji—Saudiyya

Yanzu Mata Basa Bukatar Muharrami Don Aikin Hajji—Saudiyya

Saudi Arabia embassy in Lebanon

Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah ya sanar da cewa, yanzu ba a bukatar muharrami, wanda zai zama waliyyi don raka mace yin aikin Hajji ko Umrah.

 

Dokokin kasar Saudiyya sun bayyana cewa mace tana bukatar Maharrami wanda zai kasance mahaifinta, mijinta, ko kuma dan uwanta na jini ko danta don yin aikin Hajji.

 

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a kasar Masar yayin wata ganawa da ya yi da takwaransa, ministan harkokin cikin gida na kasar Masar.

 

sun tattauna kan shirye-shiryen aikin Hajji na 2023, kamar yadda jaridar Hajj Reporters ta Najeriya ta ruwaito.

 

Da wannan sabuwar sanarwar da ta fito a ranar Litinin, yanzu mata za su iya tafiya kasa mai tsarki ba tare da muharraman su maza ba don aikin Hajji da Umrah.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci