OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaban Ma’aikata Ya mayar da martani kan yadda malamai 137 suka kasa cin Jarabawar Zama Shugabannin Makarantar sakandire

Shugaban Ma’aikata Ya mayar da martani kan yadda malamai 1

Akalla mutane 137 ne cikin ma’aikata 344 da suka zana jarabawar zama shugabanin makarantun hadin kan kasar nan guda 110 suka fadi jarrabawar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daraktoci 207 da suka ci jarabawar kwarewa ta na'ura mai kwakwalwa, an shirya yin hira da su ta baki da baki.

Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar cewa daga zango karatu na 2022/2023, wadanda za a nada shugabannin makarantu dole ne su yi jarabawar cancanta kuma dolene su ci.

A cewar wata takarda mai lamba FME/S/1317/C.1/VOL.1/51 mai kwanan wata 16 ga Agusta, 2022 mai dauke da sa hannun Daraktan Kula da Albarkatun Jama'a na Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya, David Gende,mutane 207 ne kawai Cikin 344 da aka tantance a baya suka samu nasarar cin jarabawar kwarewa ta kwamfuta kuma an shirya yi musu jarabawar baka da baki.

Abinda takardar ta ce: "Ana sa ran wadanda suka yi nasara a Gwajin da aka gudanar a ranar 16 ga Agusta, 2022, za su gabatar da kansu don yin jarabawar baki da baki." 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci