OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

NNPP Ta Zabi Kwankwaso Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyyar

NNPP Ta Zabi Kwankwaso Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam'iyya

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP).

An bayyana Kwankwaso ne a matsayin zababben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 a ranar Laraba a Abuja.

Wakilan jam’iyyar sun yanke wannan shawara ne ta hanyar sanarwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Babban taron jam’iyyar na kasa dai an gudanar ne a filin wasa na Moshood Abiola dake Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Boniface Aniebonam ya bayyana cewa taron zai bayyana kwankwaso a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

Aniebonam wanda ya bayyana a wani taron manema labarai a ranar Juma’a, 3 ga watan Yuni ya ce Kwankwason “za a tsayar da shi ba tare da hamayya ba. Kwankwaso bawan Allah ne."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci