OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Bukaci Cikakken Bincike Kan Kisan UmmuKulsum Sani

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Bukaci Cikakken Bincike Kan Ki

Geng Quanrong

Majalisar wakilan Najeriya ta ce da takaici yadda dan kasar China, Frank Geng Quanrong ya kashe wata matashiya, Ummukulsum Sani Buhari a Kano, tare da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Majalisar ta kuma yi Allah Wadai da kisan, biyo bayan amincewa da kudurin da dan majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhasan Rurum ya gabatar a gaban majalisar a Larabar nan.

Ya bukaci majalisar ta yi kira ga hukumomin tsaro su gudanar da bincike tare da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu don yi masa hukunci.

Daga nan shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ya ba da umarnin yin shiru na minti daya domin tunawa da marigayiyar, tare da bukatar babban Sufeton yansanda ya binciki zargin kisan na ta.

A larabar nan ne dai rundunar yan sandan kano ta gurfanar da Quanrong a gaban kotun majistare mai lamba 30 dake zamanta a titin zungeru dake Kano.

Kotun ta umarci a ci gaba da tsrae Quanrong gidan gyaran hali na kurmawa har zuwa 13 ga watan Oktoba kafin sake gurfanar da shi gaban kotun dake da hurumin sauraron karar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci