OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Daga Karshe Shekarau Ya Bar NNPP Ya Koma PDP

Daga Karshe Shekarau Ya Bar NNPP Ya Koma PDP

A karshe tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), ya koma jam’iyyar PDP.

Shekarau ya bayyana hakan ne da kansa a yau (Litinin) a jihar Kano yayin wani gagarumin biki da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya halarta.

Sauran masu ruwa da tsaki a wajen bikin sun hada da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyochia Ayu da dai sauran su.

Shekarau ya ce tuni ya sanar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a cikin wasika kan sauya shekar sa.

Ya bayyana cewa ya sanar da ofisoshin INEC na kasa da na Jihohi kan matakin da ya dauka na yin watsi da takarar sa na Sanata a Jam'iyyar NNPP.

Ya kara da cewa ya kuma sanar da Ofishin jam’iyyar NNPP ta kasa, jiha, kananan hukumomi da kuma unguwanni a kan matakin da ya dauka.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci