OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Da Dumi-Dumi: 'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Abba Kyari Da Wasu Mutum Hudu

Da Dumi-Dumi: 'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Abba Kyari Da Wasu Mu

DCP Abba Kyari

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana kama jami'an ta biyar wanda suka hada da Abba Kyari akan wata bakar arkalla.

 

Rundunar ta bayyana cewa tana zargin jami'an nata na da hannu cikin wata haramtacciyar fataucin miyagun ƙwayoyi, cin hanci, da kuma rashin da'a a cikin aikin su.

 

Kamen yazo ne bayan bayanan sirri sun iske shugabancin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a ranar 10 ga watan Fabrairun 2022.

 

Labarin kamen yazo ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar ranar Litinin.

 

Abba Kyari Na Fuskantar Kame Daga Amurka Yayin Da Gwamnati Ta Fara TattaunawaMalami

 

Ana iya mika tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan leken asiri, DCP Abba Kyari yayin da Gwamnatin Tarayya da Amurka suka fara tattaunawa.

 

Ministan kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN) ne ya bayyana hakan.

 

Malami ya ce gwamnatin Najeriya na tattaunawa kan yiwuwar bayar da Kyari ga Amurka bisa zargin sa da hannu wajen badakalar dala miliyan daya da wani dan damfara ta intanet, Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi ya shafa.

 

Malami wanda ya yi magana a wani shirin gidan Talabijin na Channels, ‘Politics Today' ya ce gwamnati za ta yi duk abin da za ta iya ta hanyar shari’a saboda batun ya shafi kasa da kasa da kuma cikin gida.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa babban lauyan yace, "Idan aka shiga cikin aikata laifuka, Najeriya da Amurka suna aiki tare, idan aka samu wasu laifukan da suka faru a sassa daban-daban. Don haka, Najeriya na yin abin da ake bukata ta hanyar tallafa wa abin da Amurka ke yi. yana yin hakan ne da nufin tabbatar da cewa an yi shari'ar daidai da yanayin da Amurka ke ciki, sannan kuma, a karshe, idan akwai bukatar gurfanar da su a cikin gida, babu abin da zai hana."

 

 "Haka kuma, bangarorin suna tattaunawa, suna hada kai, ana musayar takardu ta fuskar bincike, ta fuskar fitar da mai laifi, da abubuwa masu alaka."

 

Ya kara da cewa "An kafa dalilai masu ma'ana na zato kuma hakan zai haifar da yiwuwar gurfanar da shi da kuma yanke hukunci idan da gaske ya aikata laifi kamar yadda kotu ta yanke wa mutum hukunci," in ji shi.

 

Ku tuna cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta gabatar da sakamakon binciken Kyari tare da jiran martanin babban lauyan bisa ga tsarin doka ta Kasa. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci