OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Babban Kamfanin Mai Na Kasa, NNPC Ya Ce Farashin Litar Mai Naira 462 Batare Da Tallafi Ba.

Babban Kamfanin Mai Na Kasa, NNPC Ya Ce Farashin Litar Mai N

Malam Mele Kyari ya bayyana cewa farashin mai a kasar nan ya kai naira 462 batare da tallafi da gwamnati ke bayarwa ba. 

Inda ya kara da cewa kudin tan daya na mai a farashin kasuwanni duniya ya kai dala dubu daya da dari biyu da tamanin da shida ($1,283).

Kyari ya kara da cewa, kudin da ake jaza wajen rabe-raben mai a fadin kasa naira arba'in da shida ne kan duk lita daya  (N46) hadi da kudin tallafi da yakai naira dari biyu da casa'in da bakwai (N297), farashin lita daya ba mai ya zama N462 wanda jimilla a shekara yakai kudin yakai naira tiriliyan shida da biliyan dari biyar (N6.5 trillion) la'akkari da lita man fetur miliyan sittin da ake amfani a kullum.

Haka kuma, shugaban rukunin gidajen mai na gwamnati, Mallam Garba Deen Muhammad yace akwai bukatar hukumar ta sami binciken kwararu na tsawon lokaci kan adadin litar mai da ake fitarwa a rana, inda yace lissafi ka'iya kaiwa lita miliyan casa'in da takwas (N98 million) sabanin yadda aka sani a rubuce.

Wannan dai ya biyo bayan wani jawabi da shugaban hukumar shiga da fice ta kasa, Customs, kontrola janar, Hameed Ali yayi game da banbanci tsakanin kiyasin adadin mai da babban kamfanin mai na kasa, NNPC suka fitar na lita miliyan sittin, da kuma yadda suke sakar litar mai kimaminycikin gida na lita sitta  da babban mai yayi na litar mai miliyan sittin da takawas sabanin yadda ake rubutawa, wato miliyan sittin (N60 million). 


Itama anata bangaren, ministar kudi ta kasa, Hajiya Zainab Ahmad a yayin jawabin ta a gaban kwararru na musamman kan al'amuran da suka shafi rarrar mai, a ranar 18 ga watan Agusta tace kiyasin kudin da gwamnati ke warewa kan tallafi mai a kullum na kaiwa kudi kimanin naira biliyan goma sha takwas (N18.39).


"Idan akai jimillar kudaden a shekara gwamnati na kashe kudi da yakai tiriliyan shida wanda idan har aka raba zai zama kaso hamsin kenan a cikin dari.


NAN

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci