OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Buhari ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumar NNPC

Buhari ya Naɗa Sabbin Shugabannin Hukumar NNPC

kasa Muhammadu Buhari ya naɗa Sanata Margret Chuba Okadigbo a matsayin shugabar hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa, NNPC.

A wata sanarwa da mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce hakan na nufin Okadigbo ta maye gurbin Sanata Ifeanyi Ararume, wanda aka nada lokacin da shugaban kasa ya kafa hukumar a ranar 19 ga Satumba, 2021.

A cewar sanarwar, Mele Kolo Kyari shi ne babban jami’in gudanarwa, sannan Umar I. Ajiya a matsayin babban jami’in kudi.

Sauran Mambobin Hukumar sun haɗa da  Dr Tajudeen Umar daga Arewa maso Gabas, Lami O. Ahmed daga Arewa Ta Tsakiya, sai Malam Mohammed Lawal daga Arewa maso Yamma, Injiniya Henry Obih daga kudu maso Gabas), Barrister Constance Harry Marshal daga Kudu maso Kudu sai kuma a Cif Pius Akinyelure daga Kudu maso Yamma.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci