OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yara Biyu Sun Mutu Sanadiyar Ambaliyar Ruwa A Bayelsa

Yara Biyu Sun Mutu Sanadiyar Ambaliyar Ruwa A Bayelsa

Al’ummar Ogbogbene a karamar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa sun shiga tashin hankali yayin da wani yaro dan wata biyar mai suna Karina Anthony  da wata ‘yar shekara bakwai mai suna Ebiowei Rachael suka nutse a cikin ruwa.

 Wata majiya mai tushe ta shaidawa daily trust cewa Karina Anthony ya fado daga kan gado ne cikin ruwan daya mamaye dakin baccin su, yayin da Ebiowei Rachael ta nutse a cikin ruwan da ya shanye gidansu.

Jaridar daily trust ta ruwaito cewa, a kusan makwanni biyu da suka gabata, ambaliyar ruwa a jihar Bayelsa na ci gaba da karuwa, lamarin da ya jefa mazauna cikin hadari da wahala.

 Shugaban al’ummar yankin, Cif Harrish Ayemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

 Ya ce lamarin na daya daga cikin bala’o’in da ambaliyar ruwa ta jawo wa al’ummar Ogbogbene.

 Cif Ayemi ya bukaci al’ummar yankin da su cika yashi a dukkan guraben da suke bukatar hakan, inda ya koka da yadda ambaliyar ruwa ke shafar al’umma a kai a kai.

A nashi bangaren dan majalisar da ke wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Bayelsa, Honarabul Tare Porri, ya jajanta wa al’umma kan asarar da aka yi ya kuma yi alkawarin mika bukatarsu ga gwamnan jihar domin daukar matakin da ya dace.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci