OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Bindiga Sun Kutsa Wani Gari a Bayelsa, Sun Sace Basarake Da Wasu

Yan Bindiga Sun Kutsa Wani Gari a Bayelsa, Sun Sace Basarake

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari Otuabula dake karamar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa.

Bayan kai farmakin, ‘yan bindigar kimanin su 20 sun kuma yi awon gaba da wani basaraken gargajiya, wata mace mai shekaru 50 da kuma wani mutum guda.

Basaraken dai an bayyana shi da Cif Otia Isomom wanda shi ne mataimakin sarkin garin.

AllNews ya tattaro cewa an yi garkuwa da mutanen da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin.

Sauran wadanda aka sace sun hada da Misis Lucy Osain da Mista Friday Abah.

A cewar wata majiya, jirgin ruwa mai gudu ya tafi da mutanen ta hanyar ruwan garin.

Majiyar ta bayyana cewa wani ganau da aka caka masa wuka ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa ya yi sa’a da rashin kasancewa cikin wadanda aka sace.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Bayelsa ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, SP Asinim Butswat. 

Butswat ya ce tuni aka fara aikin ceto yayin da ake ci gaba da bincike.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci