OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

Umar Ardo Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Kujerar Gwamnan Adamawa a SDP

Umar Ardo Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Na Kujerar Gwamnan Adam

Dr Umar Ardo

Tsohon mai baiwa Atiku Abubakar shawara kan harkokin siyasa, Dr Umar Ardo ya lashe zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam'iyyar SDP a jihar Adamawa.

Ardo ya lashe zaben ne da kuri'u 678 daga wakilan yankuna 226 na jihar.

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jam’iyyar SDP Mustapha Jibrilla Aliyu ne ya sanar da hakan a Yola.

Aliyu ya ce, "Dan takarar daya tilo, Dakta Umar Ardo, an zabe shi ne a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben gwamna na 2023 ta hanyar tabbacin da wakilai 678 daga dukkan shiyya 226 na jihar suka yi."

Idan dai ba a manta ba Ardo ya kasance tsohon dan jam’iyyar PDP ne mai cike da takaici, inda ya rika korafe-korafen rashin tsarin dimokuradiyyar cikin jam’iyyar.

Ya kuma kai karar jam’iyyar kotu har sau 11 kan zargin da yake mata kafin ya sauya sheka.

Ardo ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar SDP bayan ya fice daga PDP.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci