OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnatin Tarayya Zata Duba Rahoton Kwamitin #Endsars – Shugaba Buhari

 Gwamnatin Tarayya Zata Duba Rahoton Kwamitin #Endsars – S

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya  zata duba rahoton da kwamitin dake da alhakin bincike kan batun #EndARS a jihar Legas ya fitar.

 

A ranar Litinin ne kwamitin bincike kan #EndSARS  ya mika rahoto kan cin zarafin da ‘yan sanda ke yi, ciki har da harbe masu zanga-zanga a Lekki ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

 

Rahoton ya bayyana cewa jami’an tsaro sun “kashe masu zanga-zangar da basa dauke da makami”.

Kwamitin ya kuma bayar da shawarwari da suka hadar da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da kuma hukunta jami’an tsaron da suka aikata laifin.

Da yake zantawa a ranar Alhamis da Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, shugaba Buhari ya ce da zarar jihar Legas ta gama duba rahoton, ita ma Gwamnatin tarayya zata karba.

Ta cikin wata sanarwa da ai mba wa Shugaban Kasa shawara kan yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar, Shugaban Kasar ya ce Gwamnatocin jihohi  za su fara daukar matakai kan rahoton kafin Gwamnatin tarayya ta yi wani abu kan shawarwarin da kwamitin ya bayar.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci