OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Atiku Ya Bada N50m Ga Yan Kasuwan Kantin Kwari da Ambaliya Ruwa Ta shafa

Atiku Ya Bada N50m Ga Yan Kasuwan Kantin Kwari da Ambaliya R

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga ‘yan kasuwar Kanti Kwari da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Kano.

Atiku ya bayyana wannan gudunmawar ne a yau (Litinin) a lokacin da yake karbar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau zuwa jam'iyyar PDP daga jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP).

Idan dai za a iya tunawa, ambaliyar ruwan ta lalata kayayyakin da darajar su ta kai na miliyoyin naira, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a jihar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kuma jajanta wa ‘yan kasuwar kan iftila'in ambaliyar ruwan da ta same su. 

A cewar sa: “Tunanin mu da addu’o’in mu suna tare da ‘yan kasuwar Kantin Kwari.

“Mun ji irin bala’in da ya afka wa kasuwar ku.

“A gaskiya muna tausaya muku, don haka nake sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 a gare su,” kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci