OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Mai Dakin Shugaban Kasar Nijar Ta Kawo Ziyarar Ta’aziyya Kano

 Mai Dakin Shugaban Kasar Nijar Ta Kawo Ziyarar Ta’aziyya

 

Mai dakin shugaban kasar Nijar, Uwargida Hadiza Mohamed Bazoum ta kawo ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Sani Dangote, wanda ya rasu a kwanan nan.

 

Mai dakin Gwamnan Jihar Kano, Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, wacce ta samu wakilcin maid akin mataimakin Gwamnan jihar Kano, Hafsat Nasiru Gawuna ce ta tarbe ta a filin jirgin Malam Aminu Kano a ranar Laraba.

 

Bayan isowar ta ne Uwargida Hadiza Bazoum ta ziyarci iyalan mamacin, inda ta ce “ ina taya ku alhinin rasuwar Sani Dangote”. A cewar ta, wannan ba rashi ne ga iyalan mamacin ko Najeriya kawai ba, ilahirin mutanen kasar Nijar na alhinin wannan rasua.

 

Maidakin shugaban kasar ta kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayi Sani Dangote, Ya sanya a Aljannatul Firdaus, kana Ya bawa iyalan sa hakurin jure rashin.

Uwargida Hadiza Bazoum ta kai ziyarar ta’aziyya ga Uban kasa, Aminu Dantata da kuma mahaifiyar marigayin, Mariya Sunusi Dantata.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci