Bola Ahmed Tinubu
Tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bebeji/Kiru ta Kano, Abdulmuminu Jibrin Kofa ya ce Bola Ahmed Tinibu zai tsaya takarar shugabancin Najeriya a kakar zabe ta 2023.
Abdulmuminu Jibrin Kofa ne ya sanar da hakan a ranar Asabar din da ta gabata yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala addu’ar shiga sabuwar shekara ta 2022 ga kasar nan.
A cewar Kofa, “A halin yanzu, babu wanda ya cancanci ya jagoranci Najeriya kamar Tinubu, idan aka yi la’akari da matsayin da yake da shi a kasar nan.
Ya kara da cewa ba sai an tallata Tinubu a APC ba.
Sama da malamai 2,500 karkashin jagorancin babban limamin Kafin-Maiyaki ne suka halarci taron addu’o’in da aka gudanar a kauyen Kofa da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano da misalin karfe 11:30 na safe.
Jim kadan bayan an gama addu’o’in, Kofa ya bayar da tallafin karatu ga mata 2,500 tare da bawa wasu matasa 2,500 tallafin bayan sun samu horo kan sana’o’i daban-daban a karkashin shirin sa.
Da yake jawabi, Kofa ya ce an gudanar da addu’o’i na musamman din ne domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da kuma samun nasarar Bola Tinubu a zabe mai zuwa.
Da yake magana kan sulhu tsakanin tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da Dr Abdullahi Umar Ganduje, Abdulmuminu Kofa ya ce, “Ba abin mamaki ba ne a ce an sulhunta Kwankwaso da Ganduje ganin cewa sun dade suna tare don haka idan aka sasanta.
Ya ce sasancin zai ciyar da Kano gaba.
0 Tsokaci