OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Kwankwaso Ya Musanta Ɓaraka Tsakanin Sa Da Shekarau

2023: Kwankwaso Ya Musanta Ɓaraka Tsakanin Sa Da Shekarau

Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Ɗan takarar Shugabancin Ƙasa, ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta ɓaraka tsakanin sa da Malam Ibrahim Shekarau.

Kwankwaso na wannan batu ne bayan rahotanni dake bayyana cewa akwai yiwuwar Shekarau zai sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP nan ba da daɗewa ba.

Ya ce babu ƙamshin gaskiya cikin labaran dake cewa an samu rashin jituwa tsakanin sa da Shekarau.

Ya kuma musanta cewa Malam Ibrahim Shekarau zai fice daga jam'iyyar ta NNPP.

“Gaskiya babu wata yarjejeniya da aka yi da ta wuce akwai buƙatu da aka kawo kuma mun yi kokarin biyansu amma ba a kawo su a kan lokaci ba.

‘Kuma babu yadda za mu iya yi musamman abin da ya shafi takara,” cewar Kwankwaso.

Kwankwaso ya ce galibin wadanda Shekarau ya kawo domin yin takara a NNPP a ƙurarren lokaci suka zo.

Ya kara da cewa INEC ba za ta amince da takarar su ba domin an kammala zaɓukan fitar da gwani.

Sai dai ya ce idan aka kafa gwamnati za'a basu muƙamai masu gwaɓi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci