OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Dan takarar Gwamna ya kalubalanci sauran 'yan takara da su gabatar da shaidar gwajin kwayoyi

2023: Dan takarar Gwamna ya kalubalanci sauran 'yan takara d

Dan takarar gwamna na jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) a jihar Katsina, Imran Ja’afar-Jino, ya kalubalanci sauran 'yan takara da su gabatar wa jama'a ingantaccen gwajin kwayoyin su.

Mista Ja’afar-Jino, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake bayyana nasa satifiket din a gaban ‘yan jarida a ranar Asabar a jihar Katsina, ya ce yana da matukar muhimmanci ga dukkan ‘yan takara su gabatar da nasu satifiket din.

Ya ce hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gwada shi kuma bata sameshi da wani sinadarin kwaya a jinin sa ba.

Ya kara da cewa bayan gwajin NDLEA, ya sake yin gwaji a babban asibitin Katsina.

Ya kuma yi kira ga sauran ‘yan takarar da su yi haka, don tabbatar da cewa ba a zabi masu shaye-shaye ba.

Mista Ja’afar-Jino ya bayyana cewa tun daga lokacin da hukumar NDLEA ta yi kira ga ‘yan siyasa da ke neman mukamai da su gabatar da kansu don yin gwaje-gwaje, da yawan su sun kasa yin hakan.

“Ina so in sanar da ku cewa, na ansa kiran da al’ummar Katsina suka yi na cewa duk wani dan takara da ya fito takara ya je a yi masa gwajin shan miyagun kwayoyi,Na yi nawa .

“Ina kira ga sauran ’yan takarar su ma su bada hadin kai a yi musu gwajin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci