OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Zamu Biya ‘Yan Najeriya Allawus Din Kudin Sifiri: Ministar Kudi

Zamu Biya ‘Yan Najeriya Allawus Din Kudin Sifiri: Ministar

Gwamnatin tarayya ta ce zata biya ‘yan kasan nan alawus din sifiri da zarar an cire tallafin man fetur.

Ministan Kudi, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan lokacin da take zantawa da gidan talabijin din channels.

Ta kara da cea tallafin man fetur din yana sa kasan nan asarar kudaden da ya kamata ace anyi amfani da su a bangaren ilimi da lafiya.

Ministan ta ce kamata yayi Najeriya ba daina biyan tallafin man fetur a gwamnatin nan cikin shekarar 2023 domin a cewar ta, tallafin gagarumar asara ce ga tattalin arzikin kasan nan.

Ko da aka tambaye ta ko gwamnatin ta shirya fuskantar tirjiya daga kungiyoyin kwadago da sauran ‘yan kasa, Hajiya Zainab Ahmed ta ce gwamnatin ta shirya samar da ababen hawa masu amfani da iskar gas su maye gurbin ababen hawa masu amfani da man fetur.

Ta kara da cewa gwamnatin tarayyar na kuma duba yiwuwar biyan alawus din sifiri ga ‘yan Najeriya na watannai shida k osha biyu domin rage musu radadin da cire tallafin ka iya kawowa.

Ta ce za’a tura kudin alawus din ne kai tsaye ga asusun bankin wadanda ya kamata da taimakon lambar shaidar banki ta BVN da kuma ta shaidar dan kasa wato NIN.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci