OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zamfara Ta Tube Sarakuna Biyu Da Hakimi Akan Tallafa Wa ‘Yan Bindiga

Zamfara Ta Tube Sarakuna Biyu Da Hakimi Akan Tallafa Wa ‘Y

Photo Source: Daily Post

Gwamnatin jihar Zamfara ta tsige wasu sarakuna biyu masu daraja ta daya da wani hakimi bisa zargin tallafa wa ‘yan bindiga.

Ana zargin shugabannin da aka sauke da taimaka wa ayyukan ‘yan bindiga da ke kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Sarakunan biyu sune Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar.

Hakimin Birnin Tsaba, Alhaji Sulaiman Ibrahim shi ne na uku a cikin wadanda aka sauke daga karagar mulki.

Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Magaji Dosara ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Gusau.

Dosara ya bayyana hakan ne bayan zaman majalisar jihar a ranar Laraba.

An kafa kwamitoci biyu daban-daban da suka binciki mutane ukun da aka dakatar bayan da aka samu rahoton cewa suna da hannu a ayyukan ta’addanci a jihar.

Majalisar ta aminta da shawarwarin da kwamitin mutum shida ya gabatar wanda ya duba sakamakon kwamitoci 2 daban-daban din da aka kafa.

Kwamitin ya kuma gano cewa sarakunan gargajiyan na cin zarafin dokar filaye ta hanyar raba filaye ba bisa ka’ida ba.

Gwamnati ta kara kwace dukkan filayen da sarakunan suka raba.

Kwamishinan ya bayyana cewa, “Majalisar zartaswar jihar ta kuma umurci ma’aikatar shari’a ta jihar da ta ba da umarnin zartarwa domin tabbatar da kudurin majalisar."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci