OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Yan sandan Filato sun kama masu laifi 178

Yan sandan Filato sun kama masu laifi 178

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta gurfanar da mutane 178 da ake zargi da aikata laifukan da suka hada da garkuwa da mutane, safara da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba hadi da ayyukan kungiyar asiri.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ne ya bayyana hakan yayin wani taro a ranar Litinin a Jos, babban birnin jihar. 

A cewar Adesina, daga cikin mutane 178 da ake zargi, an kama 118 ne a ranar 7 ga watan Yuli da laifin aikata ayyukan kungiyar asiri, a ranar da ake kaddamar da sabbin mambobin kungiyar. 

Ya ce sauran 60 din an kama su ne da wasu laifuffuka.

"Ta hanyar dabaru iri-iri da rundunar ta yi amfani da su da kuma yin amfani da kayan aiki, mun sami damar kama bata garin don tabbatar da dorewar zaman lafiya da ake samu a Filato,” inji shi.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce ya gudanar da tarurruka da dama da masu ruwa da tsaki daga yankunan da ke fama da rikici a jihar domin tabbatar da zaman lafiya.” 

“Bisa ga sahihan bayanan sirri da aka tattara, na ba da umarnin kai samame a wani gida da ake zargin maboyar kungiyar asiri ne, sakamakon haka, rundunar ‘yan sandan ‘Eagle-Eye Patrol Unit’, EEPU, ta cafke wadannan mutanen,” inji shi.

Adesina ya kuma kara da cewa a halin yanzu ana gudanar da bincike a kan dukkan wadanda ake tuhuma kuma da zarar an kammala za'a gurfanar da su a gaban kotu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci