OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

'yan sanda sun kama mutum 25 da suka karya dokar hana fita a Jos

'yan sanda sun kama mutum 25 da suka karya dokar hana fita a

Rundunar 'yansanda a jihar Filato ta ce ta kama ƙarin mutum 25 bisa zargin saɓa wa dokar taƙaita zirga-zirga da aka sanya a Jos, babban binrin jihar.

 

Kakakin rundunar 'yansandan jihar, Alabo Alfred, ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

 

A ranar Lahadi ne gwamnatin jihar ta sanya doƙar taƙaita zirga-zirga a birnin domin hana ɓata-gari shiga cikin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa domin aikata ɓarna.

 

Mista Alfred ya kuma yaba wa matasan birnin bisa yin biyayya ga dokar da gwamnatin jihar ta sanya.

 

Sai dai ya koka kan yadda wasu suka bijire wa dokar, waɗanda ya zarga da fitowa daga gidajensu suna farmakar jami'an tsaro a kasuwar Yen Tire da sauran wurare a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci