OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Sanda Sun Kama Dillalan Kwayoyi 6 a Abuja, Sun Mika Wa Hukumar NDLEA

'Yan Sanda Sun Kama Dillalan Kwayoyi 6 a Abuja, Sun Mika Wa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Abuja ta kama wasu mutane shida da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a babban birnin tarayya Abuja.

Jami’an rundunar sun kama wadanda ake zargin ne a wani samame da aka gudanar.

Kakakin rundunar a Abuja, DSP Josephine Adeh ne ta bayyana hakan.

Adeh ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun hada da Suleiman Abdulrahman Bello mai shekaru 27, Jonathan Joseph mai shekaru 35, Suleiman Shamsuddeen mai shekaru 22 da kuma Emeka Offor mai shekaru 29.

Sauran sun hada da Tanko Abdullahi da Luka Ishiaku; yan shekaru 20 da 25 kowanne.

Ta kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne dauke da dimbin tabar wiwi masu nau'uka daban-daban.

Ta kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun bayyana kwarewarsu a cikin haramtacciyar sana’ar na tsawon lokaci.

Ta kara da cewa rundunar na kara bincike domin kame wasu mutane da suke da hannu a wannan haramtacciyar sana’ar.

A halin yanzu dai an mika wadanda ake zargin zuwa hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

Adeh ta ci gaba da cewa, yayin da rundunar ta ke fada da irin wadannan laifuffuka, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gurfanar da masu aikata laifin, inda ta bukaci a tallafa wa 'yan sanda da bayanai masu amfani.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci