OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 3 Watanni da suka shude

Yan sanda sun dakile harin da aka kai gidan shugaban APC na Kano

Yan sanda sun dakile harin da aka kai gidan shugaban APC na

Rundunar yan sanda ta Kano ta dakile yunkurin wasu da ake zargin da yunkurin kai hari gidan shugaban jamiyyar APC na Kano Abdullahi Abbas. 

 

Mai magana da yawun rundunar yan sandan a Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da dakile wannan hari.

 

Kiyawa ya ce da karfe 6 na yammacin lahadin makon da ya gabata ne aka samu wasu bata gari da wannan yunkuri.

 

A cewar Kiyawa, an samu kiran gaggawa daga Chiranchi da ke karamar hukumar Gwale ta jihar a ranar 31 ga watan Mayu da misalin karfe shida na yamma. “An samu labarin cewa ‘yan daba dauke da muggan makamai suna jifan mutane da duwatsu suna kokarin shiga gidan shugaban jam’iyyar APC.”

 

Yan sandan sun ce DPO na Gwale ya tashi tawaga inda suka dakile yunkurin wadanda ake zargin.

 

Ya kara da cewa, duk da cewa ba a kama kowa ba, amma wani bincike da aka yi ya nuna cewa rikicin daba ne tsakanin wasu ’yan daba guda biyu Abdul’Yassar da Jinjiri Aljan suka shirya.

 

Sai dai basu samu nasarar kama kowa daga cikinsu ba, amma suna kokarin cafke wadanda ake zargin.

 

"Rundunar ‘yan sanda na aiki tukuru domin tabbatar da tsaron daukacin al’ummar jihar Kano" inji Kiyawa.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci