Yan Sanda sun kama wasu masu cudan takin zamani da kasa suna sayar wa manoma a Jihar Gombe.
Da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan jihar, kakakin rundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya ce a ranar 8 ga watan Yuli, 2024 ’yan sanda sun samu korafi daga wasu mazauna garin Kumo cewa sun sayi buhu 27 na takin NPK Golden akan kudi N540,000 daga wajen wadanda ake zargin saidai suna isa gonakinsusu don yin amfani da takin, sai suka gano cewa an gauraya da ƙasa.
Buhari Abdullahi, ya kara da cewa, a yayin bincikensu, wadanda ake zargin sun amsa laifin.
Sun kuma ambaci wani mai suna Shehu Shagari da ake kira Nachilo a garin Gombe a matsayin wanda ya sayar musu da takinYa ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala binciken.
0 Tsokaci