OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 13 da kwato makamai a Adamawa

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 13 da kwato maka

Nigerian Police

Akalla mutane 13 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma kwato makamai da suka hada da bindiga kirar AK-47, bindigogin gargajiya, Karamar bindiga da harsasai.

Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da kudi N358,500 da babura uku.

Da yake mayar da martani, kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, Sikiru Akande ya yaba da kokarin sauran jami’an tsaro da suka tallafa wurin kawo nasarar kamen. 

A yayin da ya bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa ‘yan sanda cikakken bayani, ya ce dole ne kowa ya hada kai domin kawo karshen matsalolin tsaro a jihar.

Akande ya kuma ba da tabbacin cewa za a gurfanar da duk wadanda ake zargin bayan an kammala bincike.

Ya ci gaba da cewa, ‘’Yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen farautar wadanda ake zargin har sai an kama su an gurfanar da su a gaban kotu."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci