OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Yan Fashi Sun Kai Hari Wani Coci A Jihar Kogi

Yan Fashi Sun Kai Hari Wani Coci A Jihar Kogi

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kai farmaki Cocin New Life Gospel da ke Sariki-Noma da ke wajen Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da wasu kudade da wayoyi da kadarorin cocin da ba a tantance ba.

 Faston cocin, Fasto Olorunfemi Ojo ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da sanyin safiyar Asabar.

Ya ce maharan wadanda adadinsu ya kai kusan 15, sun kai hari cocin ne a daidai lokacin da dattawan cocin ke shirin gudanar da sallar dare.

 Bayan haka, ya ce ’yan ta’addan sun kai wa dattawan cocin duka inda suka yi musu bulala da katako da fasassun kwalabe da duwatsu, inda suka yi musu raunuka.

 Sai dai faston ya bayyana cewa wasu ‘yan vijilanti da suke sintiri a yankin sun kawo musu dauki, inda ya ce jami’an tsaro sun kara kaimi wajen farautar barayin.

 Ya kara da cewa sun sanarda jami’an ‘yan sanda faruwar lamarin kuma tuni wasu jami’an sun je cocin domin tabbatar da irin barnar da barayin sukayi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai